Gwagware Women Empowerment and Orphans Initiative Katsina
Gwagware Women Empowerment and Orphans Initiative Katsina

A yau ne 14/9/2023 Kungiyar Gwagware Woman Empowerment and Orphans Initiative Katsina. Kar kashin Jagoranci Hajiya Rabi'atu Kabir, sun kai ziyara a gidan Alh. Yusuf Aliyu Musawa Domin taya shi murna da qara ma Juna Sani a matsayin shi na Sabon Chairman na Gwagware Foundation.

Kungiyar ta samun Jagoranci Hajiya Binta Dangani Shugabar SEMA ta Jahar Katsina, Kuma Tsohuwar Shugaba a wannan kungiya ta Gwagware Foundation, tare da Yan tawagar ta, tabbas wannan ziyara an qara sada xuminci da qara ma Juna sani.

Jawabai sun Gabata daga bakin Alh. Aliyu Muswa tare da Albishir ga Shuwagabannin kananan hukumomi na wannan kungiya, Inda yake cewa Insha Allahu wannan kungiya zata cigaba da ayyukan Alkhairin da tasaba fiye da yadda tayi a baya, na shiga lungu da saqo Domin zakulo Al'umma a taimake su Kuma a koya masu sana'ah tare da basu jari, kamar yadda wannan kungiya Mai Albarka take a baya.

WhatsApp