(Kaita LGA liason officer,) kamar yanda kuke gani sako ne da maigirma gwamna malam Dikko umar Radda yabada akai wata baiwar Allah asibiti domin nema mata magani, a karamar hukumar kaita. Wadda matar takasance mata ga marigayi malam yahaya lawal yanhoho wanda yana daya daga cikin wanda mukai hidimar maigirma gwamna dashi a gidauniyar GWAGWARE FOUNDATION yabada naira dubu dari biyar domin a kaita asibiti domin duba lafiyar ta, ta hannun Maigirma Chairman Alh Yusuf Aliyu Musawa Muna fatan Allah yasaka ma maigirma gwamna da alkhairi, Allah yakara daukaka shi.
