Gidanauniyar Gwagware foundation na cigaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin kulla kyakyawar alaka da kungiyar Dikko Radda House to House
A ranar laraba 22/11/2023 shuwagabanin kungiyar Gwagware foundation suka ziyarci ofishin kungiyar Dikko Radda House to House dake a khalilul-rahman plaza da ke acikin birnin katsina.
Shugaban Gidanauniyar Gwagware foundation Alh Yusuf Ali Musawa, wanda ya samu wakilcin sakataren gidanauniyar Hon Musa Muhammad Danmusa ya bayyana cewa dalilin wannan tattaunawar dai shine domin a kara fahimtar juna akan wannan kulla akalar aiki da za ayi tsakanin gidanauniyar da kuma kungiyar.
Da yake gabatar da jawabinsa Mai masaukin baki shugaban kungiyar Dikko Radda House to House campaign organisation Alh Saifuddeen yakubu karfi, ya bayyana farin cikin abisa amsa gayyata da shuwagabanin kungiyar sukayi domin Kara tattaunawa don samun fahimta a tsakani.
Ya ce munyi ganawa ta farko agidan shugaba, munyi ta biyu a ofishin Gidauniyar Gwagware foundation, sai muka ga ya dace mu gayyato anan ofishin namu domin ku Kara haduwa da sauran shuwagabanin mu Kuma a Kara ganawa da juna domin samun nasarar abinda aka tunkara baki daya.
Daga cikin wadanda suka halarci ganawar daga bangaren Gidauniyar Gwagware foundation akwai Hon Musa Muhammad Danmusa, Hon Shafi'u Rabiu safana daga shiyyar katsina, Alh Salisu kawari Zango daga shiyyar Daura, Hon Ibrahim kasko kankara daga shiyyar funtua sai Alh Babangida Mashi da Salim Ahmad Gaiwa
A bangaren kungiyar Dikko Radda house to house, Kuma akwai
Saifuddeen Yakubu Karfi,
Kabir Mahuta daga shiyyar Funtua, Alh Sani Mustapha daga shiyyar Daura da Alhaji Rabiu Maidabino daga shiyyar Katsina sai Mal Maryam A. Mukhtar da Alh Yusuf Jauga.
Salim Ahmad Gaiwa
P.R.O
Gwagware foundation