Gidauniyar Gwagware Foundation ta shirya wata gagarumar walimar karrama Uban Gidauniyar kuma Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda akan nasarar daya samu na zama Gwamna.
Walimar data gudana a dakin taro na Bangaren Masaukin Shugaban kasa dake Gidan Gwamnatin Jihar Katsina an kuma karrama sauran shuwagabannin kungiyar.
Da yake jawabin maraba, shugaban Gidauniyar kuma tsohon Dan takarar Mataimakin Gwamnan Alh Yusuf Aliyu Musawa yace walimar nada nufin godema Allah madaukakin sarki daya sanya Uban Gidauniyar ya zama gwamna tare da albarkacin samun mukamai masu dama ga yayan Gidauniyar.
Hon Yusuf Aliyu Musawa yace a lokacin da aka kafa Gidauniyar, ta samu nasarar tallafa marayu da gajiyayyu da masu karamin karfi da dama a ciki da wajen Jihar Katsina ta fannoni daban daban.
Da yake jawabi, Uban Kungiyar Kuma Gwamnan Jihar Katsina Mal. Dikko Radda ya bayyana ranar a matsayin mai matukar tarihi a kafuwar gidauniyar inda ya bada tabbaci cigaba da fadada ayyukan gidauniyar da tallafawa marayu da mabukata tare da gina sabuwar sakatariya ta dindindin.
Sauran wadanda sukai Magana a wajen taron sun hada da Talban musawa Hon Abdullahi Aliyu Ahmad, Alhaji Bilya Sanda, da Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar da Shiekh Abu Ammar da Alhaji Kabir Usman Amoga da Hajia Binta Husaini DanGani da sauransu.
Salim Ahmad
P.R.O
Gwagware foundation katsina